Revelation of John 17

Mace da Dabbar

1Ɗaya daga cikin malaʼiku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. 2Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”

3Saʼan nan malaʼikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. 4Macen tana saye da tufafi masu launin ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma luʼuluʼai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. 5Ga sunan da aka rubuta a goshinta:

ASIRI BABILON MAI GIRMA MAHAIFIYAR KARUWAI DA KUMA NA ABUBUWA MASU BAN ƘYAMA NA DUNIYA.
6Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu.

Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai.
7Saʼan nan malaʼikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma. 8Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za ta kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki saʼad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za ta dawo.

9“Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. 10Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma saʼad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. 11Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta.

12“Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na saʼa guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. 13Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu. 14Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna-tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.”

15Saʼan nan malaʼikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jamaʼa ce, taro masu yawa, alʼummai da kuma harsuna. 16Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. 17Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu ta yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. 18Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.”

Copyright information for HauSRK